Ru’uya ta Yohanna 3:15-17
15
Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi!
16
Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina.
17
Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara.
Settings