Ru’uya ta Yohanna 12:13-17
13
Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji.
14
Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba.
15
Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya.
16
Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa.
17
Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.
Settings