Zabura 95:1-6
1
Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2
Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
3
Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli.
4
A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5
Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
6
Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
Settings