Skip to content
Zabura 95:7-11

Zabura 95:7-11

7
gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa,
8
“Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,
9
inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.
10
Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’
11
Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options