Zabura 9:1-6
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
2
Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
3
Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.
4
Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.
5
Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin.
6
Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.
Settings