Skip to content
Zabura 89:1-15

Zabura 89:1-15

1
Maskil na Etan dangin Ezra. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai.
2
Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta.
3
Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana,
4
cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sela
5
Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.
6
Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji? Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya?
7
Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro; shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi.
8
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka? Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.
9
Kana mulkin teku mai tumbatsa; sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su.
10
Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe; da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka.
11
Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.
12
Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.
13
Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.
14
Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.
15
Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options