Zabura 73:6-11
6
Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.
7
Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.
8
Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya.
9
Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya.
10
Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.
11
Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”
Settings