Zabura 72:4-14
4
Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.
5
Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.
6
Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
7
A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
8
Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
9
Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
10
Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.
11
Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
12
Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
13
Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.
14
Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.
Settings