Zabura 72:1-11
1
Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.
2
Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.
3
Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.
4
Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.
5
Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.
6
Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
7
A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
8
Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
9
Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
10
Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.
11
Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
Settings