Zabura 68:28-35
28
Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā.
29
Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai.
30
Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.
31
Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah.
32
Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela
33
gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya.
34
Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari.
35
Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah!
Settings