Skip to content
Zabura 66:1-12

Zabura 66:1-12

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!
2
Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!
3
Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.
4
Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” Sela
5
Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum!
6
Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.
7
Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada ’yan tawaye su tayar masa. Sela
8
Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa;
9
ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi.
10
Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa.
11
Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.
12
Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options