Zabura 37:1-9
1
Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;
2
gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.
3
Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
4
Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
5
Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
6
Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.
7
Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
8
Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
9
Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.
Settings