Zabura 35:1-8
1
Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.
2
Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.
3
Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”
4
Bari waɗanda suke neman raina su sha kunya a kuma kunyatar da su; bari waɗanda suke shirya lalacewata su juya da baya su ruɗe.
5
Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;
6
bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.
7
Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami,
8
bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.
Settings