Zabura 30:1-3
1
Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda. Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.
2
Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni.
3
Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
Settings