Zabura 138:1-6
1
Ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo.
2
Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki zan kuma yabi sunanka saboda ƙaunarka da amincinka, saboda ka ɗaukaka a bisa kome sunanka da kuma maganarka.
3
Sa’ad da na kira, ka amsa mini; ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.
4
Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka.
5
Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.
6
Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai.
Settings