Skip to content

Zabura138

1
Ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo.
2
Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki zan kuma yabi sunanka saboda ƙaunarka da amincinka, saboda ka ɗaukaka a bisa kome sunanka da kuma maganarka.
3
Sa’ad da na kira, ka amsa mini; ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.
4
Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka.
5
Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.
6
Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai.
7
Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni.
8
Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options