Zabura 119:41-48
41
Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka;
42
sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka.
43
Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka.
44
Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.
45
Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.
46
Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,
47
gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu.
48
Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.
Settings