Zabura 119:33-40
33
Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.
34
Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.
35
Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki.
36
Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba.
37
Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
38
Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka.
39
Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne.
40
Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka.
Settings