Zabura 119:25-32
25
An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
26
Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka.
27
Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka.
28
Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.
29
Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.
30
Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka.
31
Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya.
32
Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata.
Settings