Karin Magana 7:6-12
6
A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka.
7
Sai na gani a cikin marasa azanci, na lura a cikin samari, wani matashi wanda ba shi da hankali.
8
Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta, yana tafiya a gefen wajen gidanta
9
da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa, yayinda duhun dare yana farawa.
10
Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi, saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.
11
(Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida;
12
wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.)
Settings