Skip to content
Karin Magana 27:17-22

Karin Magana 27:17-22

17
Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.
18
Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.
19
Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.
20
Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani.
21
Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.
22
Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options