Skip to content
Karin Magana 25:1-5

Karin Maganar da Mutanen Hezekiya Suka Kwafa: ɗaukakar Allah da Hakkin Sarki

Karin Magana 25:1-5
1
Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara.
2
Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne.
3
Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika.
4
Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa;
5
ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.