Karin Magana 11:9-14
9
Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta.
10
Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki; sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki.
11
Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin.
12
Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci, amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.
13
Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.
14
Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.
Settings