Skip to content
Karin Magana 11:1-8

Karin Magana 11:1-8

1
Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
2
Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.
3
Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.
4
Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.
5
Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu.
6
Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.
7
Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka; dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome.
8
Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala, sai ta dawo wa mugu a maimako.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options