Skip to content
Karin Magana 1:8-19

Karin Magana 1:8-19

8
Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9
Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
10
Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
11
In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
12
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
13
za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14
ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”
15
ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
16
gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.
17
Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!
18
Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu!
19
Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options