Skip to content
Karin Magana 1:1-7

Karin Magana 1:1-7

1
Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
2
Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo; don ganewa kalmomi masu zurfi;
3
don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali, kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
4
don sa marar azanci yă yi hankali, yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
5
bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora,
6
don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
7
Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options