Obadiya 1:10-15
10
Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub, za ki sha kunya; za a hallaka ki har abada.
11
A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.
12
Bai kamata ki rena ɗan’uwanki a ranar masifarsa ba, ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu, ko ki yi fariya sosai a ranar wahalarsu.
13
Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba.
14
Bai kamata ki tsaya a mararraba don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba, ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu a ranar wahalarsu ba.
15
“Ranar Ubangiji ta yi kusa don dukan al’ummai. Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku; ayyukanku za su koma a kanku.
Settings