Ƙidaya 9:9-14
9
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
10
“Gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da waninku ko zuriyarku ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Bikin Ƙetarewa ta Ubangiji.
11
Za su yi bikin da yamma, a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Za su ci naman tunkiya, tare da burodi marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.
12
Kada su bar kome daga cikinsa yă kai safe, ko a karye ƙashinsa. Sa’ad da suke Bikin Ƙetarewa, dole su kiyaye dukan ƙa’idodinsa.
13
Amma in mutumin da yake da tsarki bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi yă yi Bikin Ƙetarewar, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, domin bai miƙa hadaya ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.
14
“ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ”
Settings