Ƙidaya 3:14-39
14
Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai ya ce,
15
“Ka ƙidaya Lawiyawa bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya kowane ɗan jinjiri mai wata ɗaya ko fiye.”
16
Saboda haka Musa ya ƙidaya su duka, kamar yadda maganar Ubangiji ta umarta.
17
Ga sunayen ’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.
18
Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi
19
Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
20
Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu.
21
A wajen Gershonawa, kabilarsa su ne Libniyawa, da Shimeyiyawa; waɗannan su ne mutanen Gershom.
22
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500.
23
Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul.
24
Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa.
25
A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada,
26
da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu.
27
Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa.
28
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki.
29
Kohatawa za su yi sansani a kudu da tabanakul.
30
Shugaban kabilar Kohatawa shi ne Elizafan ɗan Uzziyel.
31
Su ne da hakkin kula da akwatin alkawari, tebur, wurin ajiye fitila, bagade, kayayyakin wuri mai tsarki da ake amfani da su a sujada, labule, da kuma kome da ya danganci aikinsu.
32
Babban shugaban Lawiyawa shi ne Eleyazar ɗan Haruna, firist. An naɗa shi a kan waɗanda suke kula da wuri mai tsarki.
33
Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari.
34
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne.
35
Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul.
36
Kabilar Merari ne aka sa su lura da katakan tabanakul, sandunanta, dogayen sandunanta, tarukanta, dukan kayan aiki da kowane abin da ya danganci aikinsu,
37
da ginshiƙai kewaye da filin tare da rammuka da turaku da igiyoyinsu.
38
Musa da Haruna da ’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi.
39
Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne.
Settings