Ƙidaya 23:8-12
8
Yaya zan iya la’anta waɗanda Allah bai la’anta ba? Yaya zan tsine waɗanda Ubangiji bai tsine ba?
9
Daga kan duwatsu na gan su, daga bisa kan tuddai na hange su. Na ga mutane da suke zaune su kaɗai ba sa ɗauki kansu ɗaya da al’ummai ba.
10
Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yaƙub ko yă ƙidaya kashi ɗaya bisa huɗu na Isra’ila? Bari in mutu, mutuwar adali ƙarshena kuma yă zama kamar nasu!”
11
Balak ya ce wa Bala’am, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka, ka la’anta abokan gābana, sai ga shi albarka kake sa musu!”
12
Bala’am ya ce, “Ba dole in faɗa abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”
Settings