Skip to content
Ƙidaya 23:1-8

Ƙidaya 23:1-8

1
Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”
2
Balak ya yi yadda Bala’am ya faɗa, sai su biyu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
3
Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun.
4
Allah kuwa ya sadu da Bala’am. Bala’am ya ce, “Na shirya bagadai bakwai, na kuma miƙa bijimi guda da rago guda, a kan kowane bagade.”
5
Ubangiji ya ba wa Bala’am saƙo ya ce, “Ka koma wurin Balak, ka faɗa masa wannan saƙo.”
6
Saboda haka, sai Bala’am ya koma wurin Balak ya same shi tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dukan dattawan Mowab.
7
Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce, “Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu. Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub; zo, ka tsine Isra’ila.’
8
Yaya zan iya la’anta waɗanda Allah bai la’anta ba? Yaya zan tsine waɗanda Ubangiji bai tsine ba?
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options