Ƙidaya 2:22-34
22
Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni.
23
Yawan mutanen sashensa 35,400 ne.
24
Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi.
25
A arewa za a sami sashen sansanin Dan, a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugabansu shi ne Ahiyezer ɗan Ammishaddai.
26
Yawan mutanen sashensa 62,700 ne.
27
Kabilar Asher ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Fagiyel ɗan Okran.
28
Yawan mutanen sashensa 41,500 ne.
29
Kabilar Naftali za su zama na biye da su. Shugaban mutanen kuwa shi ne Ahira ɗan Enan.
30
Yawan mutanen sashensa 53,400 ne
31
Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 157,600. Su ne za su zama na ƙarshe, ƙarƙashin ƙa’idarsu.
32
Waɗannan su ne Isra’ilawan da aka a ƙidaya bisa ga iyalansu. Dukansu da suke a sansani, mutane 603,550 ne.
33
Ba a dai ƙidaya Lawiyawa tare da sauran Isra’ilawa ba yadda Ubangiji ya umarci Musa.
34
Saboda haka Isra’ilawa suka yi duk ko mene ne da Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka ne suka yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu kowanne tare da kabilarsa da danginsa.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings