Skip to content
Ƙidaya 2:18-24

Ƙidaya 2:18-24

18
Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud.
19
Yawan mutanen sashensa 40,500 ne.
20
Kabilar Manasse ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur.
21
Yawan mutanen sashensa 32,200 ne.
22
Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni.
23
Yawan mutanen sashensa 35,400 ne.
24
Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options