Ƙidaya 15:37-41
37
Ubangiji ya ce wa Musa,
38
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘A dukan tsararraki masu zuwa, za ku sa tuntaye a gefen rigunarku, su sa zare mai ruwan shuɗi a bisan kowane tuntu.
39
Tuntayen za su zama muku abin dubawa don ku riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji, don kada ku bi son zuciyarku, da sha’awar idanunku yadda kuka taɓa yi.
40
Sa’an nan za ku riƙa tuna, ku kuma aikata dukan umarnaina ku zama tsarkaka ga Allahnku.
41
Ni ne Ubangiji Allahnku, da ya fitar da ku daga Masar, don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
Settings