Ƙidaya 14:13-16
13
Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji game da wannan! Da ikonka ka fitar da mutanen nan daga cikinsu.
14
Za su kuwa gaya wa mutanen wannan ƙasa. Sun riga sun ji cewa kai, ya Ubangiji, kana tare da waɗannan mutane, kuma cewa kai, ya Ubangiji, an gan ka fuska da fuska, cewa girgijenka ya tsaya bisansu, cewa kana tafiya a gabansu cikin ginshiƙin girgije da rana, da ginshiƙin wuta kuma da dare.
15
In ka kashe dukan mutanen nan gaba ɗaya, al’ummai da suka ji wannan labari game da kai za su ce,
16
‘Ubangiji ya kāsa kai waɗannan mutane a ƙasar da ya yi alkawari da rantsuwa ne, shi ya sa ya kashe su a hamada.’
Settings