Ƙidaya 11:10-15
10
Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu.
11
Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina?
12
Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu?
13
Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’
14
Ba zan iya ɗaukan dukan mutanen nan ni kaɗai ba, nauyin ya yi mini yawa.
15
In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.”
Settings