Skip to content
Ƙidaya 1:5-19

Ƙidaya 1:5-19

5
“Ga sunayen da za su taimake ku. “Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;
6
daga kabilar Simeyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai;
7
daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;
8
daga kabilar Issakar, Netanel ɗan Zuwar;
9
daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon;
10
daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;
11
daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni;
12
daga kabilar Dan, Ahiyezer ɗan Ammishaddai;
13
daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran;
14
daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel;
15
daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan.”
16
Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila.
17
Sai Musa da Haruna suka ɗauki sunayen mutanen nan da aka ba su,
18
suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye,
19
yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options