Skip to content
Ƙidaya 1:1-4

Ƙidaya 1:1-4

1
Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,
2
“Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi.
3
Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja.
4
Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options