Skip to content
Nehemiya 9:26-30

Nehemiya 9:26-30

26
“Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro.
27
Saboda haka ka miƙa su ga abokan gābansu waɗanda suka yi musu danniya. Amma sa’ad da ake danniyarsu sai suka yi kuka gare ka. Daga sama ka ji su, cikin jinƙanka mai girma kuwa ka ba su mai ceto, wanda ya fisshe su daga hannun abokan gābansu.
28
“Amma nan da nan, da suka sami hutu, sai suka sāke aikata abin da yake mugu a idonka. Sai ka yashe su ga hannun abokan gābansu don su yi mulki a kansu. Sa’ad da suka yi kuka kuma gare ka, ka ji daga sama, cikin jinƙanka kuma ka fisshe su sau da sau.
29
“Ka gargaɗe su su dawo ga dokarka, amma suka yi fariya, suka bijire wa umarnanka. Suka yi zunubi game da farillanka waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu in ya yi biyayya da su. Cikin taurinkai suka juye bayansu daga gare ka, suka zama masu taurinkai, suka kuma ƙi su saurara.
30
Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options