Skip to content
Nehemiya 9:32-37

Nehemiya 9:32-37

32
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.
33
Cikin dukan abubuwan da suka faru da mu, ka kasance mai adalci; ka yi aminci, yayinda mu kuwa muka aikata mugu.
34
Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu da kuma kakanninmu ba su bi dokarka ba, ba su ma mai da hankali ga umarnanka ko gargaɗin da ka yi musu ba.
35
Ko ma yayinda suke a masarautarsu, suna jin daɗin girmar kyautatawarka gare su, cikin ƙasar mai girma, da kuma mai fāɗin da ka ba su, ba su bauta maka ko su juye daga mugayen hanyoyinsu ba.
36
“Amma duba, mu bayi ne a yau, bayi a ƙasar da ka ba kakanninmu don su ci amfaninta da kuma waɗansu abubuwa masu kyau da take bayarwa.
37
Saboda zunubanmu, yalwar girbin da muke samu yana tafiya wurin sarakunan da ka sa a kanmu. Suna mulki bisa jikunanmu, da bisa garkenmu yadda suka ga dama. Muna cikin baƙin ciki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options