Skip to content
Nehemiya 9:15-25

Nehemiya 9:15-25

15
Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su.
16
“Amma su kakanninmu, suka yi fariya da taurinkai, ba su kuwa yi biyayya ga umarnanka ba.
17
Suka ƙi su saurare ka, suka kāsa tuna da mu’ujizan da ka aikata a cikinsu. Suka yi taurinkai, cikin tawayensu kuma suka naɗa shugaba don su koma bautarsu. Amma kai Allah ne mai gafartawa, mai alheri da jinƙai, mai jinkirin fushi, mai yalwar ƙauna. Saboda haka ba ka yashe su ba,
18
ko ma sa’ad da suka yi wa kansu siffar ɗan maraƙi, suka ce, ‘Wannan shi ne allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar,’ ko sa’ad da suka yi saɓo mai bantsoro.
19
“Saboda jinƙanka mai girma, ba ka yashe su a hamada ba. Da rana, ginshiƙin girgije bai daina bishe su a hanyarsu ba, da dare kuma ginshiƙin wuta bai daina haskakawa a hanyar da za su bi ba.
20
Ka ba da Ruhunka mai kyau don yă koyar da su. Ba ka janye Manna naka daga bakunansu ba, ka kuma ba su ruwa don ƙishirwansu.
21
Shekaru arba’in ka riƙe su a cikin hamada; ba su rasa kome ba, rigunansu ba su yage ba, ƙafafunsu kuwa ba su kumbura ba.
22
“Ka ba su mulkoki da al’ummai, kana ba su har ma da ƙasashen da suke jeji. Suka ci ƙasar Sihon na sarkin Heshbon da ƙasar Og inda sarkin Bashan yake mulki.
23
Ka sa ’ya’yansu maza suka yi yawa kamar taurarin sararin sama, ka kuma kawo su cikin ƙasar da ka faɗa wa kakanninsu su shiga su mallake.
24
’Ya’yansu maza suka shiga suka kuma mallaki ƙasar. A gabansu ka rinjayi Kan’aniyawan da suke zama a cikin ƙasar; ka ba da Kan’aniyawa a gare su, tare da sarakunansu da kuma mutanen ƙasar, su yi da su yadda suke so.
25
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options