Nehemiya 9:9-15
9
“Ka ga wahalar kakanninmu a Masar; ka kuwa ji kukansu a Jan Teku.
10
Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau.
11
Ka raba teku a gaban kakanninmu, saboda su wuce cikinsa a busasshiyar ƙasa, amma ka hallaka masu binsu cikin zurfafa, nutse kamar dutse a cikin ruwa.
12
Da rana ka bishe kakanninmu da girgije, da dare kuwa ka bishe su da ginshiƙin wuta don ka ba su haske a hanyar da za su bi.
13
“Ka sauko a kan Dutsen Sinai; ka yi musu magana daga sama. Ka ba su ƙa’idodi da dokokin da suke masu adalci da kuma daidai, ka ba su farillai da umarnai da suke da kyau.
14
Ka sanar da su Asabbacinka mai tsarki, ka kuma ba su umarnai, da farillai, da kuma dokoki ta wurin bawanka Musa.
15
Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su.
Settings