Nehemiya 2:4-8
4
Sai sarki ya ce mini, “Me kake so?” Sai na yi addu’a ga Allah na sama,
5
na kuwa ba wa sarki amsa, na ce, “In ya gamshi sarki, in kuma bawanka ya sami tagomashi a idonka, bari ka aike ni in tafi ƙasar Yahuda, birnin da aka binne kakannina, domin in sāke gina shi.”
6
Sai sarki, a lokacin sarauniya da tana zama kusa da shi, ya tambaye ni, ya ce, “Kwana nawa tafiyar za tă ɗauke ka, kuma yaushe za ka dawo?” Ya gamshi sarki ya aike ni; saboda haka na shirya lokaci.
7
Na kuma ce masa, “In ya gamshi sarki, zai yi kyau in sami wasiƙu zuwa ga gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, domin su tanada kāriya har sai na isa Yahuda?
8
A kuma ba ni wasiƙa zuwa ga Asaf, sarkin daji, yă ba ni katako don yin ƙofofin kagara na kusa da fadar haikali da kuma don katangar birni, da na wurin da zan zauna?” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.
Settings