Nehemiya 2:13-15
13
Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta.
14
Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi;
15
saboda haka na haura ta kwarin da dad dare, ina dudduba katangar. A ƙarshe, na juya na sāke shiga ta Ƙofar Kwari.
Settings