Nehemiya 13:23-29
23
Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab.
24
Rabin ’ya’yansu suna yaren Ashdod ko kuwa wani yare na waɗansu mutane, ba su kuwa san yadda za su yi Yahudanci ba.
25
Na tsawata musu na kuma kira la’ana a kansu. Na bugi waɗansu mutane na kuma ja gashin kansu. Na sa suka yi rantsuwa da sunan Allah na ce, “Kada ku ba da ’ya’yanku mata aure ga ’ya’yansu maza, ba kuwa za ku auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza ko wa kanku ba.
26
Ba don aure-aure irin waɗannan ne Solomon sarkin Isra’ila ya yi zunubi ba? A cikin yawancin al’ummai babu sarki kamar sa. Allahnsa ya ƙaunace shi, Allah kuma ya mai da shi sarki a kan dukan Isra’ila, amma duk da haka baren mata suka rinjaye shi ga zunubi.
27
Yanzu za mu ji cewa ku ma kuna yin duk wannan mugunta kuna zama marasa aminci ga Allahnmu ta wurin auren baren mata?”
28
Ɗaya daga cikin ’ya’yan Yohiyada maza, ɗan Eliyashib babban firist, surukin Sanballat mutumin Horon ne. Na kuwa kore shi daga wurina.
29
Ka tuna da su, ya Allahna, domin sun ƙazantar da aikin firist da kuma alkawarin aikin firist da na Lawiyawa.
Settings