Nehemiya 1:1-3
1
Kalmomin Nehemiya ɗan Hakaliya. A cikin watan Kisleb a shekara ta ashirin, yayinda nake a fadar Shusha.
2
Hanani, ɗaya daga cikin ’yan’uwana, ya zo daga Yahuda tare da waɗansu mutane. Na kuwa tambaye shi game da raguwar Yahudawan da suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta, da kuma game da Urushalima.
3
Suka ce mini, “Waɗanda suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta da kuma suka komo cikin yankin suna cikin babban damuwa da wulaƙanci. An rushe katangar Urushalima aka kuma ƙone ƙofofin da wuta.”
Settings