Nahum 2:1-3
1
Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki!
2
Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu.
3
Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.
Settings