Mika 4:6-10
6
“A wannan rana,” in ji Ubangiji, “zan tattara guragu; zan kuma tara masu zaman bauta, da waɗanda na sa suka damu.
7
Zan mai da guragu su zama raguwa, waɗanda aka kora, su zama al’umma mai ƙarfi. Ubangiji zai yi mulkinsu a Dutsen Sihiyona daga wannan rana da kuma har abada.
8
Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke, Ya mafaka Diyar Sihiyona, za a maido miki da mulkinki na dā, sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”
9
Don me yanzu kike kuka da ƙarfi, ba ki da sarki ne? Masu shawararki sun hallaka ne, da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda?
10
Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona, kamar macen da take naƙuda, don yanzu dole ki bar birni ki kafa sansani a filin Allah. Za ki tafi Babilon; a can za a kuɓutar da ki. A can ne Ubangiji zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.
Settings