- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Mizani mafi girma: Zina da sha’awa
Mattiyu 5:27-30
Mizani mafi girma: Zina da sha’awa
27
“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
28
Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.
29
In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
30
In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
A cikin nassin nan
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Duba kuma
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
1 Yohanna 2:16
Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.daga aya ta 28Yaƙub 1:14
amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi.daga aya ta 28Yaƙub 1:15
Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.daga aya ta 28Karin Magana 6:25
Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.daga aya ta 28Markus 9:43
In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.daga aya ta 29Markus 9:48
inda “ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a iya kashewa.’daga aya ta 29Maimaitawar Shari’a 5:18
Kada ka yi zina.daga aya ta 27Romawa 8:13
Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.daga aya ta 29Fitowa 20:17
Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”daga aya ta 28Kolossiyawa 3:5
Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.daga aya ta 292 Sama’ila 11:2
Wata rana da yamma, Dawuda ya tashi daga gadonsa, ya zaga kewaye a rufin fadansa. Daga rufin ya ga wata mace tana wanka. Matar kyakkyawa ce ƙwarai.daga aya ta 281 Bitrus 4:1
Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan.daga aya ta 29
Inda wannan ya faru



Bayanin Nazari
Settings