Mattiyu 23:4-9
4
Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.
5
“Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsufantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;
6
suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba-gaba a majami’u;
7
suna so a yi ta gaisuwarsu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’
8
“Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne.
9
Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama.
Settings